top of page

أَكَدَمِيَر هَوْسَ
AKADAMIYAR HAUSA

اَیْكِ دُوْمِن ڟِرَا دَ ݣَݣَّوَر مَكُوْمَا

Maharifiyar Ajamin Hausa

 

Yi amfani da harufa masu ƙugiya (ƙ, ɗ, ɓ) domin samun ingantacciyar harifiya. Idan kana son ka samar da alamar jã to yi amfani da ã, õ, ũ. Idan kana son sauke PDF to danna madannin Sarrafa Fayilin PDF, manhajar za ta sarrafa fayilin, bayan lokaci kaɗan ta baka mahaɗar da zaka sauke shi. Idan har ka ga sarrafawan ya ɓace kuma bai baka mahaɗin sauke PDF ba. To rubutun ne ya yi yawa, daure ka raba rubutun kashi biyu ko uku.

Stand alone diacritics may appear in several places after transliteration. You can use Ctrl + H in the word document to replace all those standalone diacritics.

ZA KA IYA TAIMAKAWA WANNAN FUROJET TA HANYAR MIƘA LITATTAFAI DA SAURAN AYYUKAN ADABI

Za ka iya miƙo mana litattafan Hausa, ko a boko, ko a ajami. Kuma za ka iya amfani da manhajarmu ka sauya litattafan Hausa boko zuwa ajami ka miƙa mana. Amman sai ka bi wannan tsari. Za ka iya yi a matsayin aikin alheri ko kuma mu bada ladar  ₦500  a kowanne littafin da ka sauya zuwa ajami kuma aka miƙo mana. 

#Adadin ayyukan adabi

Zaɓi Fayil

An samu nasarar miƙawa. Idan an zaɓi buƙatar ladar kuɗi, za`a tantance aikin da aka miƙo a yi tuntuɓa ta imel

Mungode!

An samu ero. Sake gwadawa

AYYUKA | أَيُّكَا

Kawo Kyakkyawan Canji | كَاوُوْ ݣِݣِّوَن ثَنجِے

image_xU0tNdVr_1699489254359_raw.webp
  1. ݣُرَارَ إِلِمِن بُوْكُوْ ثِكِن هَوْسَ

  2. غَغَرُمِن َ    أيْكِن فَسَّرَ جِغَجِغَن لِتَتَّفَن كِمِيَ دَ تَكَنُوْلُوْجِ

  3. سَمَر دَ ثِكَكّٜن قَمُسُن هَرشٜن هَوْسَ ثِكِن أَجَمِ دَ بُوْكُوْ

  4. سَمَر دَ لِتَتَّفَن سَنَأُوْإِ ثِكِن أَجَمِ

  5. كَفَ غِدَن هِكِمَ وَندَ زَيْ كَسَنثٜ ثِبِيَر أَيُّكَن تَرجَمَ دَ تَرَ أَيُّكَن أَدَبِ دَ كُمَ وُرِن مُهَوَرَ؞

  6. سَمَر دَ جَرِدَ، مُجَلَّ، غِدَن رٜدِيُوْ دَ تَلَبِجِن؞

  1. Kwarara ilimin boko cikin Hausa

  2. Gagarumin aikin fassara jigajigan litattafan kimiya da takanoloji

  3. Samar da cikakken ƙamusun harshen Hausa cikin ajami da boko

  4. Samar da litattafan sana'o'i cikin ajami

  5. Kafa gidan hikima wanda zai kasance cibiyar ayyukan tarjama da tara ayyukan adabi da kuma wurin muhawara.

  6. Samar da Jarida, mujalla, gidan rediyo da talabijin.

Muhimman mahaɗan adabi, ilimin kimiya da takanoloji | مُهِمَّن مَهَطَيْ

KU TUNTUƁEMUكُ تُنتُٻٜمُ

 تَرهُوْ | Tarho: (+55) 11 95557-9887

Mungode | مُنغُوْدٜ

bottom of page